Bama zawarcin Wayne Rooney-Mancini

Rooney
Image caption Sir Alex Ferguson ya ce Rooney na son barin Old Trafford

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya bayyana cewar kungiyar bata zawarcin dan kwallon Manchester United Wayne Rooney.

A ranar Laraba ne kocin United Sir Alex Ferguson ya bayyana cewar dan kwallon Ingilan mai shekaru ashirin da hudu na son barin Old Trafford.

Akan haka ne aketa alakanta Rooney din da babbar abokiyar hammayar United wato City.

Mancini yace"bamu tuntubeshi ba, kwararren dan kwallon ne, amma a yanzu ba shine matsalar ta ba".

City dai a watan Yulin 2009 ta sayi dan kwallon United Carlos Tevez ba yanda yarjejeniya tsakaninshi da Red Devils ta kare.

Da dama na ganin cewar Manchester City ce tafi dacewa da Rooney wanda yarjejeniyar da United za ta kare a kakar wasa ta 2011-12.