Shugaban Liverpool Christian Purslow ya yi murabus

Purslow da Werner
Image caption Christian Purslow (hagu) tare da shugaban NESV Tom Werner

Manajan Darektan Liverpool Christian Purslow zai sauka daga mukaminshi sakamakon sayarda kungiyar akan pan miliyan 300 ga kamfanin New England Sports Ventures (NESV).

Amma Purslow din zai cigaba da aiki a Anfield a matsayin darekta mara iko sannan kuma mai bada shawara ga sabbin masu kungiyar.

Yace"na jagoranci klub dinne don a samu masu saye sannan a fitar da ita daga kangin bashi".

Purslow ya hau kan kujerar ne a 2009,inda ya maye gurbin Rick Parry wanda ya kasance shugaba mai cikakken iko.

Shugaban kamfanin NESV Tom Werner ya ce "mun ji dadi Christian ya amince zai taimaka mana a klub din, tayin la'akari da kwarewarshi da soyayya ga Liverpool".