Tabbas Fabregas ba zai bar Emirates ba-Wenger

Fabregas
Image caption Bayan Spain ta lashe gasar kwallon duniya, da karfin tuwo aka sawa Fabregas rigar Barca

Manajan Arsenal Arsene Wenger ya ce baida tantama zai cigaba da rike Cesc Fabregas daga nan zuwa wasu 'yan shekaru a Emirates.

Kafin a fara kakar wasa ta bana ne dai, dan kwallon Spain din ya nuna muradin komawa gida ya taka leda a Barcelona.

Amma sai Gunners suka hanashi zuwa Nou Camp saboda kwangilarshi dasu sai a shekara ta 2014 zata kare.

Ana saran Barca zata kara tayin dan kwallon me shekaru 23 a karshen kaka ta bana,amma dai Wenger ya ce tabbas Fabregas ba zai bar Emirates ba.

Sau biyu dai Arsenal tana kin amincewa da tayin Fabregas daga Barca, wanda hade da Gunners din a watan Yulin 2003 daga Nou Camp.