'Yan kallo bakwai sun mutu a Kenya a ruguntsumin shiga fili

Filin wasa
Image caption Filin wasa na Nyoyo inda mutane bakwai suka mutu

Akalla 'yan kallo bakwai ne suka mutu a rungutsumin shiga filin wasa a Kenya don kallon kwallo a ranar Asabar.

Haka kuma kusan mutane ashirin na can a asibiti ranga ranga bayan aukuwar lamarin a filin wasa na Nyayo.

A cewar kungiyar bada agaji ta Red Cross, lamarin ya auku ne a filin wasan da za a kara tsakanin manyan kungiyoyin kwallo a kasar wadanda keda farin jini sosai.

Kakakin Red Cross Titus Mung'ou yace mutane shida sun mutu a wajen filin wasa lokacin da aka tattekesu a kokarin shigowa.

A buga wasanne tsakanin tsaffin abokan gaba wato Gor Mahia da AFC Leopards inda aka doke Leopards din daci daya me ban haushi.

Wakilin BBC yace jami'an tsaro sun kasa komai saboda rashin kayayyakin aiki.

Pirayi Ministan Kenya Raila Odinga ya bada umurnin ayi bincike akan lamarin