La Liga:Ronaldo ya ci kwallaye hudu, Messi yaci biyu

Ronaldo
Image caption Christiano Ronaldo yaci kwallaye takwas a wasa uku

Cristiano Ronaldo yaci kwallaye hudu a wasan da Real Madrid ta casa Racing Santander daci shida da daya, nasarar data tabatarwa da Real din jagorancin teburin gasar La Liga.

Ronaldo yaci kwallaye biyu a kowanne hutun rabin lokaci sanna sai Gonzalo Higuain da Mesut Ozil suma suka ci dai dai.

Shima Lionel Messi yaci kwallaye biyu inda ya baiwa Barcelona nasara daci biyu da nema akan Real Zaragoza.

Sakamakon sauran fafatawar:

*Getafe 3 - 0 Sporting Gijón *Almería 0 - 1 Hércules *Osasuna 3 - 0 Málaga *Espanyol 1 - 0 Levante