Fifa ba za ta saba ka'idoji ba akan batun 2018 da 2022

Zen Rufinen
Image caption Zen Rufinen ne sakatare janar na Fifa daga 1998 zuwa 2002

Hukumar dake kula da kwallon kafa a duniya Fifa ba zata amince da saba ka'idoji ba wajen rige rigen da kasashe keyi na daukar bakuncin gasar cin kofin duniya a 2018 da 2022.

A ranar Lahadin data wuce ne dai tsohon sakatare janar na Fifa Michel Zen-Ruffinen ke bayyana cewar wasu kasashe biyu masu neman damar daukar bakuncin gasar kofin duniya sun hada baki.

Hakan dai ya biyo bayan dakatar da jami'an Fifa biyu bisa zargin suna kokarin sayar da kuri'unsu.

Yace" Fifa da kwamitin da'a ba zasu bari a karya doka ba".

Wannan martanin na kunshe ne a bayanan da jaridar Sunday Times ta nuna Zen-Ruffinen wato tsohon sakatare janar na Fifa daga shekarar 1998 da 2002 wanda ya sauka bayan ya zargi Sepp Blatter cewar yana barna, sannan kuma Zen-Ruffinen din ya bayyana cewar akwai alamun Spain da Portugal da Qatar sun hada baki don sun zabi juna a 2018 da 2022.

Amma dai duka kasashen sun musanta zargin.