An janye karar da aka shigar na kalubalantar zaben NFF

Maigari
Image caption Zaben Aminu Maigari a matsayin shugaban NFF ne ya janyo takaddama

Kungiyar tsaffin kwarrarun 'yan kwallo a Najeriya wato NANF ta janye karar data shigar gaban babbar kotu a Legas na kalubalantar zaben hukumar NFF.

Janye karar dai zai taimakawa kasar kaucewa dakatarwa daga hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA.

Sakatare Janar na NFF Musa Amadu ya bayyana cewar zasu aikewa Fifa wasikar cewa an janye karar.

Fifa a ranar hudu ga watan Oktoba ta dakatar da Najeriya saboda wannan karar, inda Fifa din ta ce gwamnati na tsoma baki akan harkar kwallon kafa.

Fifa dai ta dage dakatarwar data yiwa Najeriya na wucin gadi kuma a ranar Talata za ta sake duba lamarin.