James McCarthy ya samu rauni

James McCarthy
Image caption James McCarthy zai shafe makwanni goma yana jinya

Dan wasan Wigan James McCarthy zai shafe makwanni goma ba ya taka leda sakamakon raunin da ya samu a idon sahunshi.

McCarthy, mai shekaru 19, ya samu raunin ne bayan da ya hadu da dan wasan Bolton Fabrice Muamba a wasan da suka ta shi 1-1.

"Kyata ce ta ba-gaira-ba-dalili, akwai ganganci a cikinta," a cewar kociyan Wigan Roberto Martinez.

Wannan ba karamin koma baya ba ne, ace daya daga cikin matasan da suka fi kowa kwarewa ba zai taka leda ba har tasawon makwanni bakwai".

McCarthy ya buga wasanni 11 a kakar wasanni ta bana, sai dai ya samu rauni minti 30 da fara wasansu da Bolton ranar Asabar.