Kamfanin India na gabda sayen Blackburn Rovers

Rovers
Image caption Filin wasan Blackburn Rovers

Kungiyar Blackburn Rovers ta Ingila ta ce kamfanin Venky na kasar India na gabda kamalla sayenta .

Wannan cinikin zai zamo na farko da wani kamfanin India zai mallaki kungiya a gasar premiership.

Kamfanin dai ya kware ne a harkara noman kaji da sarrafa magunguna kuma ya tattauna da Rovers da kuma hukumar dake kula da gasar premier.

Shugaban Rovers John Williams yace bangarorin biyu na saran za a kamalla yarjejeniyar daga nan zuwa watan Nuwamba.

Kungiyar ta ce anyi ganawa dalla dalla akan cinikin tare da kamfanin India.

Williams ya ce suna bin lamarin tare da taka tsantsan saboda sanin yanayin kaddarorin kungiyar.