Micheal Owen ya ji sabon rauni a kafadarshi

Owen
Image caption Micheal Owen ya cika laulayi

Dan kwallon Manchester United Michael Owen ya shaidawa BBC ya ce zai shafe makwanni yana jinya saboda sabon raunin da ya samu a kafadarshi.

Tsohon dan wasan Liverpool din kusan wata guda kenan rabonshi da ya taka leda.

A makon daya gabata ne kocinsa Sir Alex Ferguson yace dan kwallon me shekaru talatin da haihuwa ya fara horo kuma anasaran zai buga wasansu na kofin Carling tsakanin United da Wolves.

Amma sai Owen ya bayyana cewar ya samu rauni na daban a lokacin horo.

Hakan ne kuma ya sanya bai buga wasansu na daren Talata ba na kofin Carling.

Owen ya ci kwallaye 40 cikin wasanni 89 daya bugawa Ingila, kuma yawan samun rauni ya haddasa ba a kiranshi a Ingila.