An rufe filayen wasa biyu a Kenya har sai abinda hali yayi

Kenya
Image caption Pirayi Ministan Kenya Raila Odinga yana duba daya daga cikin wadanda suka raunata a filin Nyayo

Mahukunta a kasar Kenya sun rufe filayen wasan kwallo biyu a birnin Nairobi har sai abinda hali yayi sakamakon mutuwar mutane takwas wajen ruguntsumin shiga filin kwallo.

An bada umurnin rufe filin wasa na Nyayo wanda lamarin ya auku a cikinsa ranar Asabar da kuma filin wasa na City.

Shugaban hukumar kwallon Kenya Mohammed Hatmy ya shaidawa BBC cewar"haramta wasan kwallon kafa a filayen wasan biyu shine matakin da yafi dacewa".

Sai dai shugaban Fifa Sepp Blatter ya aikewa shugabanin kwallon kafa a Kenya wasikar ta'aziya saboda lamarin daya auku.

Pirayi Ministan kasar Raila Odinga ya ce zuwa karshen wannan makon za a kamalla binciken abubuwan da suka haddasa ruguntsumin.