Hodgson ya ja kunnen Man U da ta kiyayi Riena

Image caption Pepe Reina

Kocin Liverpool Roy Hodgson ya ja kunnen Manchester United game da mai tsaron gidan kungiyar Pepe Riena, inda ya ce dan wasan bana siyarwa bane.

Rahotanni a Ingila na nuni da cewa kocin Manchester United Sir Alex Ferguson na neman siyan dan wasan mai shekarun haihuwa 28.

"Idan Ferguson na neman mai tsaron gida kuma yana da kudi, zai iya cewa yana neman Pepe Reina saboda kwarewarsa." In ji Hodgson.

"Bama son mu siyarda shi saboda yana da mahimmanci a kungiyar".

Reina ya koma kungiyar Liverpool ne daga Villarreal a kan fam miliyan 6 a shekarar 2005 kuma ya buga wasanni 271 a shekaru biyar din da yayi a kungiyar.

A watan Afrailun da ya gabata dan wasan ya sa hannu a kwantaragin sake takawa kungiyar leda na tsawon shekaru shida.