Keshi ko Siasia ne zai zamo kocin Super Eagles

Image caption Samson Siasia

Hukumar kwallon kafa a Najeriya wato NFF, ta fito da jerin sunayen Stephen Keshi da Samson Siasia a matsayin wadanda za ta tantance domin zabar kocin Super Eagles.

Wani jami'in hukumar ta NFF Deji Tinubu ya shaida wa manema labarai cewa kwamitin kwararrun hukumar ne zai tantance masu horadda 'yan wasan.

Hukumar ta NFF dai ta fara tattaunawa da Samson Siasia a baya game da zama kocin na Super Eagles kafin kotu ta dakatar da jami'an hukumar bisa takaddama game da zaben su.

A yanzu dai Samson Siasia ne ke horon kungiyar Heartland da ke Najeriya, a yayinda Stephen Keshi ba shi da aikin yi tun bayan da yayi Murabus, bayan da aka kammala gasar cin kofin kasashen Afrika da aka shirya a Angola a watan Junairun bana.