UEFA za ta dauki mataki a kan Marangos

Image caption Shugaban hukumar UEFA Michel Platini

Hukumar kula da kwallon kafa ta Turai wato UEFA ta ce za ta kai tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Girka kotu, wato Spyros Marangos saboda zargin cin hanci da ya yiwa hukumar.

Mista Marangos dai ya yi zargin cewar jami'an UEFA sun karfi cin hanci ne domin baiwa Poland da Ukraine damar karban bakuncin gasar cin kofin kasashen Turai.

UEFA dai ta nemi Marangos da ya gabatar mata da hujjoji game da zargin, amma ya gagara yin hakan.

Mista Marangos dai ya shaidawa wata jarida a Jamus cewar jami'an UEFA sun siyar da damar karban bakuncin gasar cin kofin kasashen Turai a kan dala miliyan goma sha biyar.

A kwanakin baya ne dai wata jarida a Ingila ta bayyana rohotannin cewar wasu jami'an FIFA na neman sayar da kuri'unsu a zaben bada damar daukar bakuncin gasar cin kofin duniya da za a shirya a shekarun 2018 da 2022.