Ranar 2 ga Disamba za a kada kuri'a kan gasar 2018 da 2022

Fifa
Image caption FIFA ta sha alwashin daukar mataki kan zargin cinhanci

Har ila yau hukumar ta FIFA ta ce shirin kada kuri'a domin zaben kasashen da za su dauki nauyin gasar cin kofin duniya a shekarun 2018 da 2022 na nan kamar yadda aka tsara a ranar 2 ga watan Disamba.

Da farko an saran za a dage zaben bayanda aka zargin wasu manyan jami'an hukumar biyu da kokarin sayar da kuri'unsu.

Jaridar Sunday Times ta Burtaniya ce ta zargi Amos Adamu na Najeriya da Renel Tamerii na kasar Tahiti, da neman a basu kudi domin su kada kuri'unsu.

FIFA dai ta dakatar da jami'an biyu da ake zargi na wucin gadi har sai an kammala bincike.