FIFA ta janye dakatarwar da ta yiwa Najeriya

Tawagar Super Eagles
Image caption Tawagar Super Eagles ab ta taka rawar gani a 'yan shekarun nan

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta janye dakatarwar da ta yiwa Najeriya baki daya, bayan da aka janye karar da aka kai hukumar kwallon kafar kasar wato NFF.

Wani jawabi da hukumar ta fitar a ranar Juma'a, ya ce: kwamitin zartarwa na FIFA ya janye dakatarwar baki daya, bayan da ya samu tabbacin janye karar da aka kai shugabannin hukumar kwallon kafa ta Najeriyar NFF."

Abinda hukumar ta ce yanzu na nufin " Za su iya yin aiki ba tare da wani tarnaki ba."

Da farko FIFA ta dakatar da Najeriya kan abinda ta kira sanya hannun gwamnati kan harkokin kwallon kafa a kasar.

Amma sai ta janye dakatarwar na wucin gadi har zuwa ranar 26 ga watan Oktoba, abinda ya baiwa kasar damar karawa da Guinea a gasar share fagen gasar cin kofin kasashen Afrika.

A ranar Talata ne Sakataren Hukumar NFF Musa Amadu ya ce janye karar shi ne mataki na karshe da zai basu damar komawa bakin aiki.