AWC: Afrika ta kudu ta doke Tanzania

Tawagar kwallon kafan mata ta kasar Afrika ta kudu wato Bayana Bayana ta doke Tanzania da ci biyu da guda a gasar cin kofin mata ta Afrika da kasar Afrika ta kudu ke karban bakonci.

'Yar kasar Afrika ta kudu Mamphasha Popela ce ta fara zura kwallon farko ana minti 35 da wasan da aka buga a rukunin A.

Murna dai ta koma ciki ne bayan minti takwas a yayinda Esther Chabruma ta farkewa Tanzania kwallon.

Ana sauran minti hudu a tashi wasann ne kasar Afrika ta kudu ta samu bugun daga kai sai mai tsaron gida, inda Makhabe Mamello ta zura kwallon da ya ba kasar nasara.

A ranar litinin ne Najeriya wace ta lashe gasar har sau biyar a baya za ta kara da Mali a rukunin A.