TP Mazembe ta lallasa Esperance da ci 5-0

 TP Mazembe
Image caption Magoya bayan TP Mazembe na murnar nasarar da suka samu

TP Mazembe ta lallasa Esperance da ci 5-0, a zagayen farko na wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Afrika.

Ngandu Kasongo da Given Singuluma ne suka zira kwallaye biyu-biyu, sannan Alain Kaluyitika ya zira guda.

Wannan nasara ta baiwa Mazembe kwarin guiwa sosai a karawa ta biyu da za su yi a Rades, makwanni biyu masu zuwa.

Dubban jama'a ne suka cika filin wasa na Stade de la Kenya, a garin Lubumbashi, inda aka yi ta shewa da tafi ganin yadda suka murkushe Esperance wadanda su ne zakarun Afrika na 1994.

Wannan shi ne koma baya mafi muni da Esperance ta samu a tarihin gasar ta cin kofin zakarun Afrika.

Duk wanda ya lashe wannan gasar ta bana zai samu kyautar dalar Amurka miliyan daya da rabi, sannan ya wakilci nahiyar Afrika a gasar klob-klob ta duniya.