Real Madrid da Barca sun haskaka a Spain

Ronaldo
Image caption Ronaldo yana haskakawa sosai a kakar bana

Real Madrid ta doke Hercules da ci 3-1 har gida a karshen mako, abinda ya ba ta damar ci gaba da kasancewa ta daya a kan teburin La Liga da maki 23.

Ronaldo ne ya zira kwallaye biyu, yayinda Di Maria ya zira guda.

Barcelona ce dai ke biye mata baya da maki 22, bayan da ta lallasa Savilla da ci 5-0, inda Messi da David Villa suka zira kwallaye biyu-biyu.

Valencia wacce ke mataki na hudu ta tashi daya da daya tsakanin ta da Real Zaragoza.