Sneijder ya kulla sabuwar yarjejeniya da Inter

Sneijder
Image caption Sneijder ya taka rawa sosai a Inter da Holland bara

Dan wasan Inter Milan Wesley Sneijder ya kulla sabuwar yarjejeniya da klob din wacce za ta bashi damar ci gaba da taka leda har shekara ta 2015.

Dan wasan mai shekaru 26 dan kasar Holland, anta rade-radin zai koma Manchester United bayan rawar da ya taka a Inter a kakar da ta wuce.

Shi ya jagoranci Inter ta lashe gasar zakarun Turari da kuma Serie A da Coppa Italia, sannan ya kai kasarsa wasan karshe na gasar cin kofin duniya a watan Yuli.

"Sneijder ya zamo kashin bayan Inter a bara, kuma haka zai zamo bana dama shekaru da dama masu zuwa," a cewar shugaban Inter Massimo Moratti.

Rawar da dan wasan ya taka ta sa an zabe shi cikin jerin 'yan wasan da za a zabi gwarzon dan kwallon duniya a cikinsu.