Ferdinand ba zai buga wasa a gasar zakarun Turai ba

Image caption Rio Ferdinand

Dan wasan bayan Manchester United Rio Ferdinand ba zai taka leda a wasan da kungiyar za ta buga da Bursaspor a gasar zakarun ba.

Ferdinand dai bai tafi Turkiyya da sauran tawagar kungiyar ba, a wasan da za'a buga a rukunin C.

Har yanzu dai ba'a bada wani dalilin rashin tafiyan nasa ba, amma Ferdinand ya buga wasan da United ta doke Tottenham da ci biyu da nema a ranar asabar a gasar Premier.

Ferdinand, mai shekarun haihuwa 31, ya dawo taka leda ne a watan Satumba bayan raunin da ya samu a gwiwarsa a watan Yuni.

Chris Smalling ne ake kyautata zaton zai maye gurbin Ferdinand a wasan.