Westwood ya ce Woods na da sauran rawar da zai taka

Image caption Lee Westwood

Shahararren dan wasan Golf din nan Lee Westwood wanda aka nada a matsayin na daya a duniya a wasan, ya ce Tiger Woods na da sauran rawar da zai taka a wasan na Golf.

Lee West ya ce har yanzu yana ganin Tiger Woods na iya komowa na daya a duniya.

Dan Ingila Lee Westwood ya zamo na daya a duniya a gasar Golf a karon farko, abinda ya kawo karshen makwanni 281 da dan Amurka Tiger Woods ya shafe a kan matsayin. Tiger Woods mai shekarun haihuwa 34, na fuskantar kalubale a harkar golf tun bayan ya samu matsaloli a rayuwarsa wanda kuma ya yi sanadiyyar rabuwarsa da matarsa.