AWC: Kamaru ta buga kunnen doki da Equatorial Guinea

Kamaru ta buga kunnen doki da Equatorial Guinea inda suka tashi biyu da biyu a gasar cin kofin Afrika ta mata.

Kungiyoyin biyu sun buga wasan farko ne a rukunin B, kuma mai rike da kambun gasar wato, Equatorial Guinea ce ta fara zura kwallon farko a ragar Kamaru ana minti biyu da fara wasan.

Equatorial Guinea dai ta kara ta biyu ne bayan an buga minti talatin da daya a wasan.

Kamaru dai ta samu ta fanshe kwallo guda kafin a tafi hutun rabin lokaci, kuma kamaru ta farke cin da aka yi mata ne bayan an dawo hutun rabin lokaci, inda aka tashi wasan biyu biyu.

Ghana tayi galaba akan Algeria da ci biyu da guda a wasan da kungiyoyin biyu suka buga a rukunin B.