Joe Cole zai yi jinyar makwanni biyu

Image caption Joe Cole

Dan wasan Liverpool Joe Cole, ba zai samu damar taka leda ba na tsawon makwanni biyu, bayan ya samu rauni a cinyarsa.

Dan wasan ya samu raunin ne a wasan da Liverpool ta buga da Bolton a karshen makon daya gabata, kuma wannan na nuna cewar ba zai samu damar buga wasan da kungiyar za ta buga da Chelsea a ranar lahadi ba.

"Raunin bai yi tsanani ba, amma muna ganin zai yi jinya ta tsawon makwanni biyu", In ji Shugaban Likitocin kungiyar Dakta Peter Brukner.

An dai sallami Cole, a wasan shi na farko daya bugawa Liverpool a gasar Premier, kuma dan wasan ya bayyana cewa yana fuskantar kalubale a kakar wasa ta bana.