Chelsea za ta yi rashin Malouda a gasar zakarun Turai

Image caption Florent Malouda

Chelsea ba za ta samu amfani da Florent Malouda ba a wasan da kungiyar za ta buga da Spartak Moscow a gasar zakarun Turai saboda yana jinyar rauni.

Dan wasan ya samu raunin ne a wasan da kungiyar ta buga da Blackburn, a gasar Premier inda ta doke kungiyar da ci biyu da guda.

Malouda, ya zura kwallaye bakwai a gasar Premier ta bana, kuma ba zai buga wasan bane tare da Frank Lampard wanda ke murmurewa da kuma Jose Bosingwa wanda ke fama da rashin lafiya.

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya ce yana da kwarin gwiwa Malouda zai dawo taka leda a wasan da kungiyar za ta kara da Liverpool a gasar Premier ranar lahadi.