Hukumar FA ta ce bazata dauki mataki akan Redknapp ba

Image caption Harry Redknapp

Hukumar FA ta Ingila ta ce ba za ta dauki mataki a kan kocin Tottenham Harry Redknapp ba, saboda sukar da ya yiwa alkalin wasa, bayan ya amince da kwallon da Nani ya zura kungiyar a wasan da kungiyar ta buga da Manchester United a ranar asabar.

Manchester United dai ta doke Tottenham da ci biyu da nema, kuma Kocin ya yi barazanar kauracewa manema labarai muddin hukumar ta FA ta hukunta.

A baya dai hukumar ta FA ta gargadi Redknapp game da kalaman shi.

Nani dai ya zura kwallon da akayi takaddama akanta ana sauran minti shida a tashi wasan.