Redknapp ya jinjinawa 'yan wasan sa

Image caption Harry Redknapp

Kocin Tottenham Harry Redknapp ya jinjinawa 'yan wasan shi saboda bajintar da suka nuna a wasan da suka doke Inter Milan a gasar zakarun Turai.

Tottenham dai ta doke Inter Milan ne mai rike da kambun gasar da ci uku da daya.

Harry Redknapp ya ce Gareth Bale wanda ya bada kwallaye biyu da aka zura ya fi kowanne dan wasa nuna kwazo.

Kocin ya ce sauran 'yan wasan suma sun nuna tasu kwarewar, kama daga mai tsaron gida da wadanda suka zura kwallayen da kowa da kowa.

A wasan da kungiyoyin biyu suka buga a makon daya gabata, Inter Milan ce tayi nasara akan Tottenham a filin Sansiro da ci hudu da uku.