Kokarin Ingila na daukar bakunci gasar cin kofin duniya na tangal-tangal

Kokarin da Ingila take yi domin daukar bakuncin gasar cin kofin duniya a shekarar 2018 na rawa saboda binciken da wata jaridar Ingila suka yi akan wasu jami'an FIFA, kan yadda za'a yi zaben bada ikon daukar nauyin gasar.

A baya dai wani Jami'in FIFA ya ce binciken da jaridun suka wallafa ba zai shafi Ingila ba wajen zaben kasar da cancanta domin daukar bakuncin gasar.

A yanzu haka dai binciken da jaridar Sunday Times ta wallafa gama da jami'an FIFA biyu wanda suka yi zarge su da neman cin hanci kafin su kada kuri'a zaben, zai shafi yadda sauran jami'ain FIFA za su kada kuri'a a ranar 2 ga watan Disamba.

"Wannan bincike na jaridar Sunday Times, zai kawo matsala a kokarin Ingila na daukar bakunci gasar." In ji wani jami'in kwamitin neman daukar nauyin gasar na Ingila a hirarsa da BBC.

Duk da cewa dai ya rage makwanni hudu FIFA ta kada kuri'ar bada damar daukar nauyin gasar ta 2018, Jami'in ya ce Ingila bata fidda rai ba.