Najeriya ta doke Afrika ta kudu

Image caption Tawagar Falcons

Tawagar Falcons ta Najeriya ta doke Afrika ta kudu a ci biyu da guda a gasar cin kofin Afrika ta mata da kasar Afrika ta kudu ke karban bakonci.

Perpetua Nkwocha ce ta fara zura kwallon farko bayan an buga minti 22 na wasan sanan kuma ta zura na biyu ana minti 38 a wasan.

'Yar wasar kasar Afrika ta kudu Van Wyk ce ta fanshewa kasar kwallon guda, a bugun falan daya, kafin a tafi hutun rabin lokaci.

A yanzu haka dai Najeriya ce ke jogoranci a rukunin A da maki shida, bayan ta doke Mali a wasan farko da kungiyoyin biyu suka buga da ci biyar da nema.