Ban san ranar da Diaby zai dawo ba: Wenger

Diaby
Image caption Diaby yana takawa Arsenal leda sosai a baya-bayan nan

Kociyan Arsenal Arsene Wenger ya ce bai san ranar da Diaby zai dawo taka leda ba, biyo bayan raunin dan wasan ya samu.

Dan wasan mai shekaru 24, rabansa da ya taka leda tun ranar 16 ga watan Oktoba, bayanda ya kasa warkewa daga raunin da Paul Robinson na Bolton ya ji masa.

Tun bayan nan kuma an yiwa dan wasan tiyata har sau biyu, abinda yasa Wenger ya ce: "Bamu san tsawon kwanakin da zai dauka ba - dole ne mu yi hakuri.

Ya dai taba karyewa a kafa a watan Mayun 2006, amma ya warke inda ya ci gaba da takawa Arsenal leda sosai.