Rooney zai je Amurka domin jinya

Rooney
Image caption Rooney ya dade yana fama da rauni

Dan wasan Manchester United Wayne Rooney zai je Amurka domin yin jinya da atisayi kan raunin da yake fama da shi a idon sahun shi.

Dan wasan mai shekaru 25, ba zai buga wasan United da Manchester City ba, kuma ba a saran zai kara taka leda sai nan da makwanni uku.

Rooney zai yi atisayin ne a filin wasa na kamfanin Nike a Oregon.

"Zai iya zuwa can ba tare an sa masa ido kamar yadda za a sa masa anan ba," a cewar mataimakin kociyan Manchester United Mike Phelan.

Ya kara da cewa: "yana bukatar zuwa can. Kuma dukkan mu mun amince da hakan".

Dan wasan na Ingila ya bada mamaki lokacin da sanya hannu kan sabuwar kwantiragin shekaru biyar a United, kwanaki biyu bayan ya bayyana cewa yana son barin kungiyar.