Asamoah Gyan ya taimakawa Sunderland

Image caption Asamoah Gyan

Asamoah Gyan ya zura kwallaye biyu a wasan da kungiyarshi ta Sunderland ta doke Stoke City da ci biyu da nema.

Wasan da Gyan ya buga shine na farko da aka fara da shi a gasar Premier tun da Sunderland ta sayo shi.

An sallami dan wasan Stoke City Ryan Shawcross a wasan.

A makon daya gabata dai Sunderland din ta sha kashi a hannu Newcastle da ci biyar da daya.