Man City ta fafardo bayan ta doke West Brom

Mario Balotelli ya zura kwallaye biyu a wasan da Manchester City ta doke West Bromich Albion da ci biyu da nema.

An sallami Balotelli a wasan bayan ya tokari Youssuf Mulumbu, sannan daga baya aka sallami Mulumbu bayan ya tade Tevez

Kafin wasan dai Manchester City ta sha kashi a wasanni uku a jere, abin daya kuma ya sa kocin kungiyar ya fara fuskantar matsin lamba daga magoya bayan kungiyar.