Arsenal ta sha kashi a hannu Newscastle

Image caption Andy Carroll bayan ya zura kwallon

Newscastle United ta doke Arsenal a filin Emirates da ci daya mai ban haushi.

Andy Carroll ne ya zura kwallon dab da kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Arsenal dai ta barar da kwallaye da dama a wasan, kuma ana cikin karin lokaci ne aka nunawa dan wasanta Laurent Koscielny jan kanti, saboda ya turgude dan wasan Newscatle.

A yanzu haka Arsenal ta koma a matakin na uku ne a tebur a gasar ta Premier.