An fidda Ghana a gasar cin kofin Afrika ta mata

Image caption Equatorial Guinea ta lallasa Ghana

Mai rike da kambun gasar cin kofin Afrika ta mata Equatorial Guinea ta tsallake zuwa wasan kusa dana karshe a gasar cin kofin Afrika ta mata.

Equatorial Guinean dai ta tsallake zuwa matakinne bayan ta lallasa Ghana da ci uku da guda a wasan da kungiyoyin biyu suka buga a rukunin B.

Equatorial Guinea ce dai ta jagoranci rukunin B , sannan kuma Kamaru ta zamo na biyu bayan ta doke Algeria da ci biyu da daya.

A Yanzu haka dai mai daukar masaukin baki, kasar Afrika ta kudu zata fafata ne da Equatorial Guinea a wasan kusa dana karshe, sai kuma Kamaru da zata kece raini da Najeriya.