CAF ta sanya 'yan Ghana 3 a takarar zakaran dan kwallon Afrika

Image caption Asamoah Gyan

Asamoah Gyan na daya daga cikin 'yan wasan Ghana uku da suka samu shiga jerin sunayen 'yan takarar lashe kyautar zakaran dan kwallon Afrika na shekarar 2010.

Sauran 'yan wasan Ghanan da suka samu shiga jerin 'yan wasan goma da Hukumar CAF ta fitar sun hada da Andre Ayew da kuma Kevin Prince Boateng.

Wadannan 'yan wasan za su yi takarar da Samuel Eto'o na kasar Kamaru da 'yan wasan Ivory Coast biyu, wato Didier Drogba da kuma Solomon Kalou.

Harwa yau akwai 'yan wasan kasar masar biyu Mohamed 'Geddo' Nagy da kuma Ahmed Hassan.

Eto'o, ya lashe kyautar har sau uku daga shekarar 2003-2005, kuma ya taimakawa Inter Milan lashe gasar zakarun Turai a watan Mayu.

Drogba, wanda ya lashe kyautar a shekarar 2006 da kuma 2009, ya taimakawa Chelsea lashe gasar Premier ta Ingila a bara.

Sunayen 'yan wasan da ke takarar kyautar zakaran dan kwallon Afrika.

Andre Ayew (Marseille/France, GHA), Kevin-Prince Boateng (AC Milan/Italy, GHA), Madjid Bougherra (Rangers/Scotland, ALG), Didier Drogba (Chelsea/England, IVC), Samuel Eto'o (Inter Milan/Italy, CMR), Asamoah Gyan (Sunderland/England, GHA), Ahmed Hassan (Al-Ahly/EGY), Salomon Kalou (Chelsea/England, IVC), Seydou Keita (Barcelona/Spain, MLI), Mohamed 'Geddo' Nagy (Al-Ahly/EGY)

Sunayen 'yan wasan zakaran dan kwallon Afrika na cikin gida.

Oussama Darragi (Esperance/TUN), Michael Eneramo (Esperance/Tunisia, NGR), Ahmed Hassan (Al-Ahly/EGY), Dioko Kaluyituka (TP Mazembe/DRC), Mohamed 'Geddo' Nagy (Al-Ahly/EGY)