Haile Gebrselassie ya yi murabus

Image caption Haile Gebrselassie

Wanda ya kafa tarihi a gudun dogon zongo Haile Gebrselassie ya bada sanarwar daina tsere.

Dan tseren mai shekarun haihuwa 37 wanda kuma dan asalin kasar Ethiopia ne ya bada sanarwar ne bayan ya kasa kammala gudun dogon zangon New York, saboda rauni.

"Ban taba tunanin zan daina tsere ba, amma ina ganin wannan shi ne karo na farko da nayi tunanin ajiye aiki, kuma na ga ina bukatar in huta". In ji Gebrselassie.

Gebrselassie ya kafa tarihin gudun dogon zango a duniya a shekarar 2008.

"Bari kuma in nemi wani aikin," ya kara da cewa . "Ya kamata in ba matasa dama su ma su taka tasu rawar a fagen tsere."