Ronaldo ya karbi kudin diyya daga jaridar Daily Telegraph

Image caption Cristiano Ronaldo

Real Madrid star Cristiano Ronaldo ya karbi kudin diyya daga jaridar Daily Telegraph dake Ingila, game da wani kara daya shigar kan cewa jaridar ta bata mashi suna.

Jaridar dai ta wallafa wani labari ne a watan Yulin shekarar 2008 inda ta zargi dan wasan da ganganji bayan an ganshi a wani wurin shakatawa yana rawa a lokacin dayake jinya.

A lokacin da jaridar tayi zargin dai, Cristiano na takawa Kungiyar Manchester United leda.

Jarida dai tace Cristiano ya ajiye sandar dayake dogarawa ne domin rawa da wasu mata uku.

Jaridar dai ta amsa laifin batawa dan wasan suna kuma ta nemi ahuwa, amma harwa yau kotu ta bukaci jaridar ta da ta biya Cristiano kudin diyya.