An kori bukatar da City ta shigar kan Balotelli

Image caption Mario Balotelli

Hukumar FA ta Ingila ta kori karar da Manchester City ta shigar kan jan katin da aka baiwa Mario Balotelli a wasan da kungiyar ta buga da West Brom a karshen makon da ya gabata.

A yanzu haka dai, Balotelli ba zai buga wasanni uku a gasar Premier ba a jere, ciki harda wasan 'yan gida daya da City za ta kara da United a ranar Laraba.

An nunawa dan wasan jan kati ne bayan ya tokari Youssuf Mulumbu a wasan da kungiyar ta doke West Brom biyu da nema.

Har wa yau dai hukumar ta FA ta yi watsi da karar da Arsenal ta shigar domin neman sauya katin da aka nuwa dan wasanta Laurent Koscielny a wasan da Newcastle ta doke ta da ci daya da nema.

A yanzu haka dai, dan wasan ba zai buga wasanni biyu a jere ba.