Drogba na fama da zazzabin cizon sauro

Image caption Didier Drogba

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya ce Didier Drogba na fama da zazzabin cizn sauro, amma ya fara murmurewa.

Kocin ya ce bai san yadda Drogba ya samu cutar ba, saboda babu irin ta a Ingila.

Anceloti ya ce Drogba zai samu buga wasan da kungiyar za ta buga da Fulham a ranar Laraba.

Drogba dai ya fara zazzabin ne a ranar jajiberin karawar da Chelsea ta yi da Liverpool, inda ta sha kashi da ci biyu da nema.