Ferguson na nuna shakku game da karawar United da City

Image caption Sir Alex Ferguson

Manchester United na fuskantar kalubale game da shirin da take yi na tunkarar kungiyar Manchester City a gasar Premier ta Ingila.

Yawancin 'yan wasan Manchester United dai na jinyar raunin da suka samu, a yayinda wasu ke fama da mura.

Kocin United Sir Alex Ferguson ya ce Ryan Giggs da Owen Hargreaves ba za su samu buga wasan ba, sannan akwai shakku a kan Nani.

"A gaskiya bani da kwarin gwiwa cewa Nani zai samu buga wasan, saboda yanayin da yake ciki." In ji Ferguson.

"Wasu daga cikin 'yan wasan mu da dama na fama da mura, bamu san iya nawa ne za su iya buga wasan ba."

Ana dai kyautata zaton Paul Scholes da Dimitar Berbatov da kuma Nemanja Vidic suna cikin 'yan wasan dake fama da mura.