Faransa ta fito da 'yan wasa 23 don karawa da Ingila

Image caption 'Yan wasan Faransa

Dan wasan Barcelona Eric Abidal na cikin 'yan wasa 23 da Koci Laurent Blanc ya kira domin taka leda a wasan sada zumunci da Faransa za ta buga da Ingila a filin Wembley.

Abidal, mai shekaru 31, na daya daga cikin 'yan wasa biyar da hukumar kwallon Faransa ta tuhuma game da nuna rashi da'a da wasu 'yan wasan suka yi a gasar cin kofin duniya da kasar ta halarta a Afrika ta kudu a watan Janairu da ya gabata.

Abidal dai bai fuskanci fushin hukumar kwallon kafar ba, amma dai hukumar ta dakatar da Patrice Evra da Nicolas Anelka.

'Yan wasan da aka kira:

Masu tsaron gida: Cedric Carrasso (Bordeaux), Hugo Lloris (Olympique Lyon), Steve Mandanda (Olympique Marseille).

'Yan wasan baya: Anthony Reveillere (Olympique Lyon), Gael Clichy (Arsenal), Philippe Mexes (AS Roma), Adil Rami (Lille), Mamadou Sakho (Paris St Germain), Bacary Sagna (Arsenal), Eric Abidal (Barcelona).

'Yan wasan tsakiya: Alou Diarra (Bordeaux), Yohan Cabaye (Lille), Yoann Gourcuff (Lyon), Yann Mvila (Stade Rennes), Samir Nasri (Arsenal).

'Yan wasan gaba: Karim Benzema (Real Madrid), Kevin Gameiro (Lorient), Guillaume Hoarau (Paris St Germain), Florent Malouda (Chelsea), Loic Remy (Olympique Marseille), Mathieu Valbuena (Olympique Marseille), Dimitri Payet (St Etienne).