Mataimakin kocin Chelsea Ray Wilkins ya bar kungiyar

Image caption Ray Wilkins tare da Carlo Ancelotti

Kungiyar Chelsea da ke Ingila ta bada sanarwar cewa ba zata sabonta kwantaragin mataimakin kocin kungiyar ba, wato Ray Wilkins, kuma zai bar kungiyar nan take.

An nada Wakilins ne a matsayin mataimakin kocin kungiyar a farkon shekarar 2009, kuma ya yi aiki tare da Luiz Felipe Scolari da Guus Hiddink da kuma Carlo Ancelotti.

Shugaban Kungiyar Ron Gourlay ya ce: "Munawa Ray godiya kan ayyaukan da yayi a kungiyar kuma muna mishi fatan alheri.