Ancelloti ya kalubalanci jan katin da aka baiwa Essien

Image caption Carlo Ancelotti

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya kare dan wasansa Michael Essien, inda ya ce dan wasan bai cancanci jan katin da aka nuna mishi ba a wasan da kungiyar ta doke Fulham da ci daya da nema.

Micheal Essien ya tade Clint Dempsey da kafa biyu a lokacin da aka yi karin lokaci.

"Banji dadin matakin da alkalin wasa ya dauka ba," In ji Ancelloti.

"bai yi niyyan raunata dan wasan ba, domin ya bi kwallo ne."

Shiko Kocin Fulham Mark Hughes cewa ya yi, "Essien ya kai harin ne da mugunta, kuma jan kantin da aka nuna mishi ya dace".

Essien ne dai ya zura kwallon da Chelsea ta ci a wasan, a wasan shi na farko bayan ya gama jinya.