'Yan takarar gasar gwarzon dan kwallon kafar BBC

Gwarzon dan wasan Afrika

BBC ta fitar da sunayen 'yan wasa biyar da za su fafata a gasar zaben gwarzon dan kwallon kafa na Afrika a shekarar 2010.

'Yan wasan su ne:

  • Asamoah Gyan
  • Andre 'Dede' Ayew
  • Samuel Eto'o
  • Yaya Toure
  • Didier Drogba

Za ku iya zaben gwarzonku domin ya samu nasara daga yanzu zuwa 10 ga watan Disamba mai zuwa, sannan kuma a sanar da wanda ya lashe gasar ran 17 ga watan Dismba.

Za ku iya zaben ne ta hanyar latsa rariyar likau din da ke biye:

http://www.bbc.co.uk/worldservice/africa/2010/11/101111_afoy_2010_vote_page.shtml

Ko kuma ku aike da sakon text zuwa +44 7786200070.

Wannan kambun mai daraja da kima shi kadai ne kambun da magoya bayan 'yan wasa ke tantance wanda zai lashe shi.

Wasu kwararru da suka fito daga sassa daban-daban na nahiyar Afrika ne suka zabo 'yan wasan da ke takarar.

Mai gabatar da shirin wasannin BBC Fastrack, Farayi Mungazi, ya ce: "Wannan shekarar ta kasance shekara ce mai matukar muhimmanci ga wasan kwallon kafa a nahiyar Afrika, inda yankin ya dauki nauyin gasar cin kofin duniya a karon farko, kuma kasar Angola ta dauki nauyin gasar cin kofin Afrika.

"Matasan kasar Ghana sun kawata gasar ta cin kofin duniya, a don haka abun farin ciki ne da aka samu 'yan kasar Ghana suka samu shiga takarar a karon farko tare da gwarzayen 'yan wasa Eto'o da Drogba da kuma Toure."

Wanda ya yi nasara a shekarar da ta gabata shi ne Didier Drogba na kulob din Chelsea da kasar Ivory Coast, bayan kwallayen da ya jefa wa kulob dinsa da kuma kasarsa.

Wadanda suka lashe gasar ta gwarzon dan kwallon kafar BBC na Africa a baya sun hadar da:

2009 - Didier Drogba

2008 - Mohamed Aboutrika

2007 - Emmanuel Adebayor

2006 - Michael Essien

2005 - Mohamed Barakat

2004 - Jay Jay Okocha

2003 - Jay Jay Okocha

2002 - El Hadji Diouf

2001 - Sammy Kuffour

2000 - Patrick Mboma