TP Mazembe ta lashe gasar zakarun Afrika a karo na hudu

Image caption Mazembe ce ta lashe gasar da aka shirya a bara

TP Mazembe ta buga kunnen doki ne da Esperance, inda kungiyoyi suka tashi daya da daya a kasar Tunisia a bugu na biyu da kungiyoyin suka yi a wasan karshe na cin kofin zakarun Afrika.

A wasan farko da suka buga a Congo, TP Mazembe ce ta lallasa Esperance da ci biyar da nema.

Esperance ta nemi, tayi yinkurin rama kwallaye da Mazambe ta zura mata a wasan farko, amma ta gagara yin hakan.

Mazembe ce ta lashe gasar da aka shirya a bara, kuma a yanzu zata samu kyautar dala miliyan daya da rabi, kuma itace zata wakilci nahiyar Afrika a gasar cin kofin zakarun kungiyoyin duniya.