Ancelotti ya koka da mumunar rawar da Chelsea ta taka

Image caption Carlo Ancelotti

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya ce rawar da kungiyar ta taka a wasan da Sunderland ta doke ta da ci 3-0 a filin Stamford Bridge, ya fi muni a tsawon wa'adinsa a kungiyar.

A yanzu haka dai maki biyu ne ya raba Chelsea da Arsenal wacce ke mataki na biyu, kuma an doke ta ne a karo na uku a kakar wasan bana a gasar Premier.

"Zamu hadu ranar Alhamis bayan an gama buga wasannin sada zumunci na kasa da kasa, domin yin nazarin abin da ya faru." In ji Ancelotti.

Chelsea bata samu amfani da John Terry da kuma Frank Lampard saboda rauni, a yayinda Michael Essien na fuskantar dakatarwa bayan jan katin da aka nuna mishi, a wasan da kungiyar ta buga da Fulham.