Haye ya musunta zargin cin hanci

Image caption David Haye

Zakaran daben WBA David Haye ya karyata zargin da ake yi mai na caca kafin damben dayayi da Audley Harrison a ranar asabar.

A zargin David Haye da tabbatarwa wa 'yan caca cewar zai doke Audley Harrison a zagaye na uku. Hukumar kula da wasan dambe ta duniya dai ta harantawa 'yan dembe caca.

David Haye dai ya ce baya bukatar yin caca, saboda ya san zai samu isashen kudi a demben da yayi.