Dan Najeriya zai shugabanci Chelsea

mai horas da 'yan wasan Chelse

Kulob din Chelsea ya daga likkafar dan Najeriya Michael Emenalo daga matsayinsa na mai nemo 'yan wasa zuwa mataimakin babban mai horar da 'yan wasan kulob din.

Emenalo, wanda ya ke tare da kulob din na Chelsea tun watan Oktoban shekarar 2007, ya maye gurbin Ray Wilkins ne a matsayin, kuma kulob din na Chelsea ya ce ya samu matsayin ne saboda kwazonsa.

Emenalo mai shekaru 45, ya buga wa Najeriya kwallo a gasar cin kofin duniya ta shekarar 1994, ya kuma buga wa kulob din Notts County kwallo na wani dan takaitaccen lokaci a tsakiyar shekarun 1990.

Zai dai ci gaba da nema wa kulob din 'yan wasa, yayinda yake ci gaba da bunkasa kwarewarsa a harkar horar da 'yan wasa.