Gerrard ba zai taka leda ba na tsawon makwanni hudu

Image caption Steven Gerrard

Kyaftin din Liverpool Steven Gerrard ba zai samu damar taka leda ba na tsawon makwanni hudu, bayan raunin da ya samu a wasan sada zumuncin da Ingila ta buga da Faransa a ranar Laraba.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 30 ya taka leda ne a wasan na tsawon minti 84.

"Steven ya samu rauni a cinyarsa," In Ji babban likitan kungiyar Dokta Peter Brukner.

"Bayan mun gwada shi ne muka gano cewa ya samu rauni a cinyarsa, kuma ina ganin ba zai samu damar taka leda ba na tsawon makwanni hudu." In ji Brukner